✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: Ranar Alhamis Kotun Ƙoli za ta saurari shari’ar

Ranar Alhamis Kotun Ƙoli za ta saurari shari'ar Zaɓen Gwamnan Kano.

Kotun Ƙoli ta sanya Alhamis din nan a matsayin ranar da za ta saurari shari’ar Zaɓen Gwamnan Jihar Kano.

Daya daga cikin lauyoyin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, Bashir Tudun Wazirci, ya tabbatar da samun takardar da Kotun Ƙoli ta aiko na sanar da su ranar da zaman shari’ar zai kasance.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na Jami’yyar NNPP ne ya daukaka kara zuwa Kotun Ƙoli bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta kwace kujerarsa ta ba wa dan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

Rubutaccen hukuncin Kotun Ƙolin dai dai ya tabbatar da Abba a matsayin wanda ya yi nasara, sabanin hukuncin da alkalai suka karanta a kotu.

Wannan tufka da warwarar na daga cikin abubuwan da yake ƙalubalanta.

Yana kuma ƙalubalantar hukuncin kotun daukaka kara na soke zaɓen sa bisa hujjar cewa shi ba ɗan jami’yyar NNPP ba ne.

Da farko Abba Kabir Yusuf ya je kotun ɗaukaka karar ce bayan da farko Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano ta soke zaɓen ta ba ayyana Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara.

Kotun farko ta soke zaben ne bisa hujjar karancin kuri’u, bayan da ta soke masa kuri’u sama da 160,000 cewa ba hasastattu ba ne, saboda rashin sitamfi da sa hannun baturen zabe a jikinsu.

Daga bisani dai lauyoyin NNPP sun bayyana cewa kuri’u kimanin 1,800 ne APC ta gano ba su da sitamfi, don haka kuri’un da kotun farkon ta soke sun zarce abin da ya kamata.