Dan takarar Gwamnan Jihar Osun na Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya jefa kuri’arsa.
Sanata Adeleke ya kada kuri’a ne da misalin karfe 9 na safe a rumfa ta tara, mazaba ta biyu da ke Karamar Hukumar Abogunde Saga Ede ta Kudu.
- Osun: Jihar da aka fara ‘inconclusive’ a Najeriya za ta sake zaben Gwamna
- Duk wanda ya ba mu kudi za mu karba, mu zabi wanda muke so —Mutanen Osun
- Fada ya barke tsakanin mayakan Ansaru da ’yan bindiga a Birnin-Gwari
Karo na biyu ke nan da Sanata Adeleke ya fito neman kujerar Gwamnan Jihar, kuma suna bugawa da Adegboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC kuma gwamna mai ci.
A zaben 2018 INEC ta bayyana Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’a 255,505 inda ya kada Adeleke mai kuri’a 255,023 bayan an yi zabe zagaye na biyu a wasu rumfunan zabe bakwai a wasu kananan hukumomi hudu.
An yi zagaye na biyu a lokacin ne bisa zargin magudi da cin zarafin masu zabe.
An yi zagaye na biyu ne bayan da farko a zaben da ba a kammala ba Adeleke na kan gaba da tazarar kuri’a 353 bayan ya samu kuri’a 254,698, Oyetola kuma na da 254,345.
INEC ta ce zaben bai kammala ba ne saboda yawan kuri’u da aka soke ya fi tazarar da ke tsakanin kuri’un ’yan takarar yawa.
Yanzu dai ga shi sun sake haduwa a akwatin zabe, kuma ana ganin Sanata Adeleke na da kishirwan ganin ya kada Mista Oyetola domin huce haushi.