✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben gwamnan Kebbi bai kammala ba —INEC

tazarar kuri'un da ke tsakanin manyan 'yan takarar zaben 45,278 bai kai kuri'un da aka soke ba

Hukumar INEC ta bayyana cewa zaben Gwamnan Kebbi bai kammala ba, sakamakon yawan aringizo da soke kuri’u da aka samu a 20 daga cikin kananan hukumomi 21 da ke jihar.

Baturen zaben, Farfesa Yusuf Sa’idu daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwao, ya ce duk da cewa jam’iyyar APC mai mulkin jihar ce ke kan gaba wajen yawan kuri’u, tazarar kuri’un da ke tsakanin manyan ‘yan takarar zaben 45,278 bai kai kuri’un da aka soke ba.

Ya kara da cewa APC ta samu 388,258, PDP kuma 342,980, daga kuri’u 760,438 da aka kada a zaben.

Ya bayyana cewa kuri’un da aka soke sun kai 91,829, wanda ya haura tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar.

An samu sahihan kuri’u 792,234 da kuma lalattatu 18,204 a zaben.