✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Edo: Tsakanin Obaseki da Ize-Iyamu wa zai kai bantensa?

A ranar Asabar ce za a yi ta ta kare a karon battar da aka faro tsakanin manyan jam’iyyun siyasar Najeriya na APC da PDP…

A ranar Asabar ce za a yi ta ta kare a karon battar da aka faro tsakanin manyan jam’iyyun siyasar Najeriya na APC da PDP a zaben Gwamnan Jihar Edo.

Gwamna mai ci, Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP da babban mai kalubalantarsa Fasto Osagie Ize-Iyamu na Jam’iyyar APC za su san makomarsu.

Masu zabe za su yanke hukuncin wa suke so ya shugabcnci jihar a matsayin Gwamna a shekara hudu masu zuwa.

Takarar tasu tana haifar da zaman dardar a jihar Edo a tsakanin manyan jam’iyyun siyasar biyu da kuma ita kanta kasa.

Hakan ya sa kasar Amurka ta ce za ta sanya takunkumin hana biza ga duk wanda ya haifar da matsala ko tashin hankali a lokacin zaben, kamar yadda ta sanya ga wadanda suka aikata haka a zaben jihohin Kogi da Bayelsa a bara.

Musayar jam’iyya

Dambarwar siyasa a Jihar Edo a tsakanin ’yan takarar biyu da suka yi musayar jam’iyyu a bana, ta faro ne tun shekara hudu da suka gabata.

A lokacin da Fasto Ize-Iyamu ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar PDP, yayin da Gwamna Obaseki ya tsaya a karkashin APC kuma ya samu nasara.

Sai dai tabarbarewar dangantaka da aka samu a tsakanin Gwamna Obaseki da tsohon ubangidansa a siyasa, tsohon Gwamnan Jihar kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamaret Adams Oshiomhole ta jawo hana shi tikiti a jam’iyyar APC wanda hakan ya tilasta shi komawa PDP wadda ta ba shi tikitin yi mata takara.

Shi kuma Fasto Ize-Iyamu ya koma APC wadda ya kalubalanta a zaben 2016, kuma ta tsayar da shi takara a zaben na da ke tafe.

Zazzafar adawa

Tunda ’yan takarar biyu suka bayyana ake samun zafafan kalamai da muhawarori da caccakar juna ba a tsakaninsu kadai ba, hatta a tsakanin jam’iyyunsu da magoya bayansu.

Zaben dai sake fafatawa ne a tsakanin abokan hamayya biyu da suka fafata a baya, inda Fasto Ize-Iyamu ke neman fanshe kayen da ya sha.

Shi kuma Gwamna Obaseki yana neman yi wa Ize-Iyamun kaye a karo na biyu.

A baya dai da kyar da jibin goshi Obaseki ya kayar da Ize-Iyamu wanda babban fasto ne a cocin Redeem Christian Church of God (RCCG).

Ya kuma taba zama Sakataren Gwamnatin Jihar Edo da kuma Shugaban Ma’aikata Gidan Gwamnatin Jihar.

Oshiomohole ya sauya ra’ayi

Kwamaret Oshiomhole ya taka rawa sosai wajen tallata Gwamna Obaseki a zaben 2016 tare da kushe Ize-Iyamu.

Sai dai a wannan karo ya rika bi lungu da sakon jihar yana cewa ya zo ne don ya gyara kuskurensa na tallafa wa Obaseki ya zama Gwamnan Jihar.

Ba ta tsaya a Edo ba

Sai dai fafatawar ba ta tsaya a tsakanin al’ummar jihar kadai ba, inda a farkon wannan mako aka ruwaito Mai Gwamna Obaseki Shawara kan Watsa Labarai, Mista Crusoe Osagie, yana caccakar tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu tare da bayyana cewa ba zai samu damar fadada daular siyasarsa zuwa Edo ba.

A cewarsa mutanen Edo ne ke da ikon zaben wanda zai zama ubangidansu a jihar.

Wata sanarwa ya fitar a Benin babban birnin jihar ya ce: “Wani rahoto da aka watsa a kafafen labarai ya ja hankalinmu inda tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

“A kokarinsa na mamaye siyasar Jihar Edo, ya umarci mutane a kan wanda za su zaba ya jagoran ce su nan da shekara hudu masu zuwa.

“Tsohon Gwamnan na kokarin mamaye siyasar Edo inda yake son kakaba siyasar ubangida kamar yadda ya shafe shekaru yana yi a Jihar Legas da jihohin Kudu maso Yamma.

“Mutanen Edo a shirye suke su kawo karshen siyarsa kama-karya ta ubangida,” inji sanarwar.

INEC ta kammala shirye-shirye

Tuni dai Hukumar INEC ta ce ta gama kintsawa don gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, yayin da aka tura ’yan sanda dubu 31 don tabbatar da an yi zaben cikin kwanciyar hankali.