✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben APC: Tinubu da Osinbajo sun ja layi

Yunkurin samar da dan takarar shugaban a jam'iyyar APC daga yankin Kudancin Najeriya ta hanyar masalaha ya faskara.

Yunkurin samar da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC daga yankin Kudancin Najeriya ta hanyar masalaha ya faskara.

Aminiya ta gano cewa manyan ’yan takara biyu daga yankin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da kuma Uban Jam’iyyar APC na Kasa kuma Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu sun ja daga.

Iyayen jam’iyyar masu ci da kuma tsofaffi da sauran masu-fada-a-ji daga yankin sun yi ta kokarin samar da dan takarar jam’iyyar ta hanyar masalaha, amma abin ya gagara.

Hakan ta faru ne bayan Gwamnoni 10 na jam’iyyar daga yankin Arewa sun sanar da janyewar yankinsu daga neman tikitin takarar shugaban kasa, inda suka nemi  a tsayar da dan yankin Kudu.

Sun kuma ba wa gwamnonin Kudu wuka da nama wajen tsayar da dan takarar ta hanyar masalaha gabanin babban taron zaben dan takarar da jam’iyyar za ta fara gudanarwa daga ranar Litinin 6, wa Laraba 8 ga watan Yuni da muke ciki a Abuja.

Wannan kuma na zuwa ne bayan zaman da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi da gwamnoni da sauran masu-fada-a-ji na jam’iyyar kan bukatar jam’iyyar ta tsayar da dan takarar da zai iya lashe mata zaben 2023.

Masu kokarin ganin an yi sasancin da suka hada da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Cif Bisi Akande, tare da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba da gwamnoni da kuma dattawan yankin, sun gana da masu neman takara daga yankin Kudu maso Yamma a gidan Osoba kan wannan batu na masalaha.

Ko a watan jiya, Cif Bisi Akande da Cif Olusegun Osoba sun yi wata ganawa da masu neman takarar daga yankin, inda suka yi ittifakin gudanar da yakin nemn zabensu ba tare da jin mutuni ko tayar da rikici ba.

A ranar Asabar, bayan dawowar Buhari daga kasar Ghana ya bukaci daukacin masu neman takarar da su tattauna a tsakaninsu kan yiwuwar fitar da dan takara tilo babu hamayya, gabanin zaben tsayar da dan takarar jam’iyyar.

Buhari ya yi wannan kira ne bayan gwamnonin yankin Arewacin Najeriya sun bukace shi da ya nemo magajinsa daga yankin Kudu.

Zuwa ranar Lahadi, Buhari ya ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki kan batun, inda ya yi zama da Kwamitin Mashawartar Jam’iyyar APC na Kasa.

Mahalarta zaman da ya gudana da Fadar Shugaban Kasa sun hada da Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan da Cif Akande da magajinsa, Tsohon Shuaban Jam’iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun da shugaban jam’iyyar mai ci, Sanata Abdullahi Adamu.

Shi ma Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Snaata Iyiola Omisore da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum; Filato, Simon Lalong; Zamfara, Bello Matawalle da David Umahi na Jihar Ebonyi, sun halarci zaman na ranar Lahadi.

Bayan taron, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce ya ce a lokacin taron, Buhari ya yi batu ne kan yiwuwar faitar da dan takarar da zai kai APC ga nasararta ta uku a jere daga babban zaben 2015.

Buhari ya ce, “Na yi imanin ganawar da muka yi da kuma sauya tunaninmu za su karfara tsari dimokuradiyya a cikin jam’iyyarmu.

“Na riga na yi zama da gwamnoninmu da manyan mambobin jam’iyya da ke burin samun tikitin takara shugaban kasa a babban zbaen 2023.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa an yi nasara a zaman da muka yi kuma hakan ya nuna jam’iyyarmu ta shirya domin samun nasara a karo na uku a jere bayan zaben shugaban kasa na 2015.”

Aminiya ta gano cewa an yi zaman ne da zummar duba yiwuwar tsayar da dan takara babu hamayya daga cikin mutum 23 da suka nuna sha’awar yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Majiyoyinmu sun shaida mana cewa a yayin da zaman ke gudana, Osinbajo da Tinubu, kowannensu ya nuna alamar ba zai hakura ba, inda suka ci gaba da tuntuba tare da neman goyon bayan daliget.

Masu neman takarar daga yankin Kudu maso Yamma su ne Osinbajo, Tinubu, da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole da kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da takwaransa na Jihar Ogun, Dapo Abiodun da Sanata Robert Ajayi Boroffice da Fasto Tunde Bakare.

Majiyarmu ta ce sauran masu neman takarar sun nuna alamar za su iya sauya ra’ayi, amma Osinbajo da Asiwaju sun nuna ba za ta sabu ba.

“Muna sa ran Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa ne za su fafata saboda kokarin da aka yi na shawo kansu ya ci tura,” inji wata majiya da ta bukaci a boye sunanta.

Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin Cif Akande da Cif Osoba, hakarmu ba ta cimma ruwa ba, sun ki cewa uffan kan batun sasancin.

Daraktan Yada Labaran Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce jam’iyyar na fatan a gudanar da babban taro da zaben dan takara cikin gaskiya da adalci da kuma nasara.

“Za mu gudanar da babban taro da zai kasance cikin gaskiya da adalci; kowa na neman samun kuri’u daga daliget a zaben tsayar da dan takarar,” kamar yadda ya bayyana.

Daga Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Abdullateef Salau, Muideen Olaniyi (Abuja), Abiodun Alade (Legas), Mumini AbdulKareem (Ilorin), Nabob Ogbonna (Abakaliki), Abubakar Sadiq Mohammed (Zariya), Ahmed Mohammed (Bauchi) & Salim Umar Ibrahim (Kano)