Alkalin kotun lardin Georgia a kasar Amurka ya yi watsi da karar da shugaban kasar, Donald Trump ya shigar a kan kuri’un mutanen da ba su halarci rumfar zabe ba.
Kungiyar yakin neman zaben Trump ta shigar ta karar tana neman kotun da ta yi aiki da dokar kuri’un da aka kada ba tare da an halarci rumfar zabe ba.
Shugaban na Amurka, ya samu kansa cikin yanayi na tsaka mai wuya bayan da abokin karawarsa Joe Biden ya tsere masa a yawan kuri’u a zaben da zuwa yanzu ake ci gaba da kirgawa a kasar.
Zaben Amurka na 2020 ya bayar da mamaki ta fuskoki da dama ta yadda ake ganin akwai yiwuwar Trump ya bi sahun shugabannin kasar da suka sha kaye a yunkurinsu na yin tazarce duba da yadda abokin hamayyarsa kuma tsohon mataimakinsa, Joe Biden, ya yi masa fintinkau.
A hannu guda kuma ana ganin Biden, wande ke neman shiga sahun shugabannin Amurka mafiya yawan shekaru a duniya na fuskantar barazanar sake karawa da tsohon maigidan nasa a zagayen zabe na biyu, muddin ya kasa samun kaso 270 na kuri’un da aka jefa.
Zaben na bana ya bayar da mamaki ta wasu fuskoki ta yadda Trump ya sha kaye a wasu yankunan da ya samu tagomashi a zaben baya, shi ma Biden ke fuskantar kalubale a wasu yankuna da a baya jami’yyarsa take tunkaho da su.