Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, ya bukaci magoya bayansa da sauran al’ummar Jihar da su kwantar da hankalinsu yayin da aka shiga halin rashin tabbas kan sakamakon zaben Jihar.
Fintiri, wanda kuma shi ne dan takarar PDP ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi ga manema labarai ranar Lahadi, lokacin da yake tsokaci a kan sakamakon.
Da sanyin safiyar Lahadi ce dai Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar, Malam Hudu Yunusa Ari, ya ayyana ’yar takarar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben, duk da ba a kammala tattara shi, kuma ba shi ya kamata ya ayyana shi ba.
Amma a cewar Gwamna Fintiri, dama tun a zaben farko ya fahimci take-taken wasu jami’an hukumar na tadiye shi, duk kuwa da acewarsa, alamu sun nuna shi ya tasamma lashe zaben.
Ya ce, “An fara tattara sakamako cikin nasara da Kananan Hukumomi 11, kafin a dakatar da shi, saboda za a dawo a ci gaba da misalin karfe 11:00 na safe.
“Amma muna cikin jira sai Kwamishinan zabe ya yi gaban kansa wajen bayyana sakamakon zabe, aikin da ba nasa ba ne a doron doka, kuma haramtacce ne.
“Wannan abin takaici e, yunkuri ne a tayar da zaune tsaye. Amma duk da haka, ina kira da a kwantar da hankula. A matsayina na shugabanku, zan tabbatar babu wanda ya yi wa Dimokuradiyya zagon kasa.
“Tuni hedkwatar INEC ta kasa ta nesanta kanta daga wannan kwamacalar, sannan ta sha alwashin yin abin da ya dace. Abin da kawai ya dace a wannan yanayin shi ne a kammala tattara sakamakon wanda halastaccen mai bayyana sakamako, Farfesa Mele Kyari zai jagoranta.
“Ina kira da kowa ya kwantar da hankali, domin za mu ci gaba da fafutuka har sai mun yi nasara. Abin da kawai INEC za ta yi a wannan yanayin ta tsira da mutuncinta shi ne ta yi adalci,” in ji Fintiri.