Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Kimiyya da Fasaha ke fadin kasar nan, gabanin shiga zaben 2023.
Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya bayar da wannan umarni a wata takarda mai dauke da sa hannun wani jami’in ma’aikatar, I.O Folorunsho.
Wasikar wacce aka raba wa manema labarai a Abuja, an aika da ita ne zuwa ga Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE), Idris Bugaje.
Ministan, ya bukaci a isar da wannan umarnin ga Shugabannin Makarantun Kimiyya da Fasaha domin dakatar da harkokin karatu daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris, 2023.
Wasikar ta ce: “Saboda matsalolin tsaro da ka iya shafar ma’aikata, dalibai, da kuma dukiyoyi a cibiyoyinmu, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, bayan tattaunawa mai zurfi da jami’an tsaro da abin ya shafa, ya umarci rufe dukkanin makarantun Kimiyya da Fasaha.
“Kuma za a dakatar da harkokin karatu daga ranar Laraba, 22 ga Fabrairu zuwa ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023.”
Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta bayar da umarnin rufe jami’o’in kasar nan domin bai wa dalibai damar shiga zabukan da za a yi a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris.