Kasar Amurka ta ware Dala miliyan 50 a matsayin gudunmawarta ga Najeriya a babban zaben da za ta gudanar a shekarar 2023 mai zuwa.
Hakan ya fito ne daga bakin Jakadan Amurkar a Najeriya, Mista Will Stevens a jawabin da ya gabatar yayin wani taron horar da ’yan jarida wanda Cibiyar Horas da ’Yan jarida Afrika ta Yamma (WABMA) ta shirya a Ibadan a ranar Litinin.
- Gwamnatin Amurka ta bukaci jami’anta su fice daga Abuja
- Gwamnatin Amurka ta bukaci jami’anta su fice daga Abuja
Jakadan ya kuma ce gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa (USAID), domin ganin an yi adalci a zaben.
Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden da kasar za ta bayar har da horar da ’yan jarida kan aikinsu da kungiyoyin fararen hula.
Sannan kuma za a taimaka wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.