Yanzu haka shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP sun shiga taro domin fitar da wanda zai tsaya Mataimaki ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar.
Ana sa ran jagororin za su samar da matsaya daga wadanda kwamitin Janar Aliyu Gusau (mai ritaya) ya tantance a matsayin wadanda suka cancanta.
- Tun da nake ban taba faduwa zabe ba — Tinubu
- Shugaban Masu Rinjaye da na Marasa Rinjaye a Majalisar Dattijai sun ajiye mukamansu
Wadanda kwamitin ya tantance dai sun hada da Gwamnoni uku daga Kudu maso Kudancin kasar nan, da suka hada da Nyesom Wike (Ribas) da Ifeanyi Okowa (Delta) da Udom Emmanuel (Akwa Ibom).
Wadanda suka halarci taron da Mataimakin Shugaban mambobin kwamitin daga Arewa, Umaru Damagun, ke jagoranta sun hada da Gwamna Samuel Otom da Aminu Tambuwal da Bala Muhummad da tsohon Gwamna Babangida Aliyu.
Sauran sun hada da Sule Lamido da Liyel Imoke da Olusegun Mimiko da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Ndudi Elunelu.
Gabanin shiga taron dai, Shugaban jam’iyyar na kasa Dokta Iyorchia Ayu ya bukaci taron ya samar da mafita ga jam’iytar tsakanin Laraba zuwa Juma’a.
Ya ce: “Dan takararmu na Shugaban Kasa Atiku ya rubuto mana takarda kan a matsayinmu na shugabannin jam’iyya mu fitar masa da Mataimaki.
“Dan takarar namu ya yanke shawarar yin tafiya da kowa ba kamar zaben 2019 ba, da bai dogon nazari ba a zaben abokin takara,” inji Shugaban na PDP.