Minista a Ma’aikatar Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya gargadi ’yan Najeriya da su guji yin kalaman batanci ga gwamnati, yana mai cewa sam hakan bai dace ba.
Ministan ya yi gargadin ne sakamakon wasu kalaman rashin dattaku da ke fitowa daga wasu ’yan kasar.
Sanarwa da daraktan yada labaran ma’aikatar, Henshaw Ogubike, ta ce Matawalle, ya bukaci ’yan kasar su ba da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya, hakuri da hadin kai da kuma sanin kalaman da za su furta, domin samun cigaba mai dorewa a Najeriya.
Ya ce “Irin wadannan maganganun na tada hankali ne da firgici kuma hakan na iya ta’azzara tashe-tashen hankula tare da zaman dar-dar a cikin al’umma.”
Ministan ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana da manufa mai kyau don haka yana aiki ba dare ba rana wajen ganin Najeriya ta gyaru ta zama kasa mai kyau.
- Basunu: Zuriyar Hausawa da ba sa jin Hausa a Ibadan
- Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da Najeriya —Aminu Dantata
Da yake magana kan tattalin arzikin kasa, Matawalle ya ce Tinubu na da kyakkyawar fahimtar alakar rashin tsaro da talauci don haka gwamnatinsa ke kara tallafa wa masu kananan sana’o’i, baya ga shirin tallafa wa magidanta miliyan 15 masu karamin karfi.
Bugu da kari, ministan ya ce Shugaba Tinubu yana iya bakin kokarinsa wajen magance matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ministan ya kara da cewa: “ba da jimawa ba, shugaban kasar ya amince da kafa wani kwamiti wanda ya hada da gwamnonin jihohi da wakilan tarayya kan kafa ’yan sandan jihohi da za su taimaka wajen yaki da ayyukan bata gari.”
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai, inda ya bayyana cewa abin da ya shafi dan Najeriya daya ya shafi al’ummar kasar baki daya.