✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da Najeriya —Aminu Dantata

Shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin shugabancin firaminista shi ne mafi alheri ga kasar nan.

Shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin shugabancin firaminista da wasu ’yan majalisa suke nema shi ne mafi alheri ga kasar nan.

Dantata, ya bayyana haka ne a lokacin da wasu yan majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.

Aminu Dantata ya ce, “Na gode da wannan ziyara, kuma ina yi wa wannan gagarumin gangami addu’ar samun nasara.

“Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da kasar nan saboda babu kashe kudin gudanarwa kaman tsarin shugaban kasa da muke bi.

“Ina fata za ku samu goyon bayan abokan aikinku, kuma ina rokon Allah Ya ba ku basira, Ya kuma yi muku jagora wajen cimma wannan kyakkyawan manufa ta taimakon kasar nan.

Karin bayani na tafe……