Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ’yan Majalisar Wakilai da su daina yawan yi wa ministoci da shugabannin hukumomin Gwamnatin Tarayya kiranye da titsiye su kan ayyukan da suke gudanarwa.
Tinubu ya yi wannan roƙo ne yayin jawabinsa a wurin buda bakin da aka shirya wa ’yan Majalisar Wakilan ranar Laraba a Abuja.
Shugaban ya ce duk da cewa sa ido yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin mulki, gayyato jami’ai fiye da kima na iya firgitasu ya kuma kawo cikas a tasirin ayyukan da za a yi wa ‘yan Najeriya.
Ya bukaci ‘yan majalisar da su nuna kwarewa wurin gudanar da ayyukansu na sa ido.
- An mayar da Gaza maƙabarta mafi girma a duniya — EU
- Majalisa Za Ta Gayyaci Emefiele Kan Bashin N30trn Da Gwamnatin Buhari Ta Karɓa
“Ina ganin yadda kwamitoci daban-daban su ke kiran ministoci da shugabannin hukumomi. Na kai kuka ga Shugaban Majalisa da cewa a bar talaka ya sarara.
“A bari mutanen nan su yi aikinsu. Ba ina cewa ba ku da tasiri ba ne, ba kuma ina cewa ku daina sa ido akan ayyukan da ake yi a ma’aikatu ba ne, roƙon da nake yi shi ne, ku barsu su yi aiki.
“Amma ku yi la’akari da aikin da kowace hukuma da ma’aikatanta ke yi. Kamar ayyukan da ke kan Gwamnan Babban Bankin ko kuma Ministan Tattalin Arziki na Kasa da Kudi da sauran al’umma baki ɗaya.
“Idan hankalinsu ya zama ba a kwance ba ko kuma suna kidime, to abubuwan ba za su tafi yadda kowa ke so ba, watakila sai kun fara zaman majalisa har cikin dare.
“Dole ne mu nemo hanyar da za mu zaunar da juna. Wannan roƙo ne gare ku. Ku duba yiwuwar amincewa da wakilan shugabannin ma’aikatu da ministoci a wasu lokuta ko ma takardu.”
Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda Majalisar Dokokin ke ayyukanta.
Ya kuma jaddada godiya da jin daɗinsa akan yadda ake samun jituwa tsakanin bangaren zartarwa da Majlisar dokoki.
Ya ce, kyakkyawar alaƙar da ke tsakani ta ba majalisar damar amincewa da kudurorin bangaren zartarwa da a yanzu ‘yan Najeriya ke mora.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Wakilan, Tajudeem Abbas, ya jaddada muhimmancin yin afuwa da karamci, da addu’a a cikin watan Ramadan, ya kuma yi kira da a hada kan al’umma da kuma goyon bayan Shugaba Tinubu.
“Ina so in yi kira gare mu da mu yi amfani da wannan wata wajen ƙara ayyukan alheri da kuma rage munanan ayyuka,” in ji shi.
Da yake tsokaci kan watanni 10 na wannan gwamnati, Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas ya bayyana cewa bangaren zartarwa da na majalisar dokoki sun ci gaba da aiki tare domin ci gaban kasa.
“Ya zuwa yanzu dai, majalisar na goyon bayan Shugaban Ƙasa da manufofinsa, kuma za mu ci gaba da tabbatar da cewa mun yi aiki tare,” in ji Tajudeen Abbas.