Firaministan kasar Haiti, Ariel Henry ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban gwamnatin yankin Caribbean.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Mohamed Irfaan Ali, shugaban Guyana kuma shugaban kungiyar Caribbean Community (CARICOM) ya fitar.
“Mun amince da murabus dinsa bayan kafa kwamitin shugaban kasa na rikon kwarya da kuma nada firaminista na rikon kwarya,” in ji Ali, yana gode wa Henry kan hidimta wa kasar Haiti da ya yi.
Bayanai sun ce wannan sabon lamarin ya bar gibin zaben shugaba tun bayan kisan da aka yi wa shugaban kasar na karshe a shekarar 2021.
- Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin Tinubu
- Yadda Za Ku Yi Girke-Girken Azumi Da Kuɗi Kaɗan
Henry mai shekaru 74 a duniya ya mika takardar murabus dinsa ne bayan shugabannin CARICOM sun gudanar da wani taron gaggawa kan halin da ake ciki a kasar Haiti inda rikicin da kungiyoyin ‘yan daba ke jagoranta ya haifar da rudani.
Murabus din na Henry na zuwa ne bayan da shugabannin yankin suka gana da safiyar jiya Jamaica da ke kusa da kasar, domin tattaunawa kan tsarin mika mulki, wanda Amurka ta kira a makon da ya gabata da a “gaggauta” tare da kafa Majalisar Shugaban Kasa yayin da gungun bata gari suka yi kira ga Henry ya yi murabus.
Henry ya tafi Kenya ne a karshen watan da ya gabata domin tabbatar da jagorancin tawagar tsaro ta kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya don taimakawa ‘yan sanda yaki da ‘yan fashi da makami.
Sai dai wani mummunan tashin hankali da ya barke a babban birnin Port-au-Prince a lokacin da ba ya nan ya yi sanadiyar makalewarsa a yankin Puerto Rico.