✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus

Mataimakiyar ta sanar da murabus ɗinta a zaman majalisar na ranar Litinin.

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko, ta ajiye muƙaminta.

Ta bayyana murabus ɗinta ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Litinin a Birnin Benin, babban birnin jihar.

Oligbi-Edeko, wadda ke wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa Maso Gabas II, ta ce ta yi murabus ne, saboda jam’iyyarta ta PDP ta rasa rinjaye a majalisar bayan wasu ’yan jam’iyyar ciki har da Shugaban Majalisar sun koma jam’iyyar APC.

An zaɓe ta a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar karo na takwas a ranar 16 ga watan Yunin 2023, kafin ta yi murabus.

Bayan ta yi murabus, majalisar ta zaɓi Mista Osamwonyi Atu daga jam’iyyar APC (Orhionmwon ta Gabas) a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Jagoran Majalisar, Hon. Jonathan Aigbokhan, ya gabatar da ƙuduri cewa a ci gaba da biyanta dukkanin haƙƙoƙinta da ke tattare da kujerar mataimakiyar shugaban majalisar.

Wannan ƙuduri ya samu goyon bayan shugaban ’yan adawa, Hon. Charity Airobarueghian, kuma dukkanin ‘yan majalisar sun amince da shi.

A cikin wasiƙar murabus ɗinta, Oligbi-Edeko ta ce ta yi hakan ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da daidaito ga dukkanin mazaɓu.

Ta kuma gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP saboda damar da suka bata ta wakilci mazaɓarta.

’Yan majalisar sun yaba da ƙoƙarinta da jajircewarta wajen yi wa jama’a hidima.