✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa ya ajiye muƙamin nasa ba.

Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.

Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ya aike da takardar murabus ɗinsa kimanin makonni biyu da suka wuce, inda ya ce dalilansa na ƙashin kai ne.

Har yanzu ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus ɗin ba.

An naɗa Baba-Ahmed a watan Satumban 2023 a matsayin mai bai wa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan harkokin siyasa.

A lokacin da yake riƙe da muƙamin, ya wakilci gwamnati a taruka da dama na ƙasa da na siyasa.

Sai dai ya sha suka a shekarar 2024, bayan da ya samu saɓani da Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, kan kalaman da suka shafi Ƙungiyar Tsofaffin Shugabannin Arewa (NEF), inda ya taɓa zama kakakinta kafin naɗinsa.

“Sukar NEF da Matawalle ya yi bai dace ba. Ya fi dacewa ya bayyana irin gudunmawar da ministocin Arewa da sauran jami’an gwamnati irina ke bayarwa wajen inganta tsaro da rage talauci a yankin,” in ji Baba-Ahmed

Matawalle ya mayar da martani da cewa: “Dukkanin wanda Shugaba Tinubu ya naɗa, ciki har da Dokta Baba-Ahmed, na da alhakin kare da kuma tallata ayyukan wannan gwamnati a fannoni daban-daban.”

Baba-Ahmed wanda ya taɓa zama Shugaban Ma’aikata na tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sananne ne wajen tsayawa kan gaskiya da adalci a harkokin ƙasa.

Kafin naɗin nasa, ya kasance Daraktan Yaɗa Labarai na ƙungiyar dattawan Arewa.

Tsohon babban jami’in gwamnati ne daga Jihar Kaduna kuma sananne ne a matsayin dattijo mai kishin Arewa.

Murabus ɗinsa ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a tsakanin masu bibiyar al’amuran siyasa a Arewa.