Kwamishinan Kula da Ayyuka da Tantancewa na Jihar Kano, Muhammad Diggol, ya ajiye aikinsa bayan ya miƙa takardar murabus ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Murabus ɗin Diggol na zuwa makonni kaɗan bayan an sauya masa ma’aikata daga Ma’aikatar Sufuri zuwa Ma’aikatar Kula da Ayyuka da Tantancewa.
- Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato
- ’Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Katsina, sun sace iyalansa
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus ɗin nan take.
An fara naɗa Injiniya Muhammad Diggol a matsayin Kwamishinan Sufuri a farkon gwamnatin Gwamna Abba, a shekarar 2023.
Daga baya, aka tura shi zuwa Ma’aikatar Kula da Ayyuka da Tantancewa, inda ya ci gaba da aiki har zuwa lokacin da ya yi murabus.
Gwamnan, ya gode wa Diggol saboda jajircewarsa, himma da kyakkyawan ayyukansa yayin kasancewarsa a cikin Majalisar Zartarwar Jihar.
Hakazalika, Gwamnan ya masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.