Mata magoya bayan Sanata Muhammad Ali Ndume sun yi barazanar yin zanga-zanga tsirara a Majalisar Dokoki ta Kasa, idan ba a mayar da shi kan shugabancin kwamitocin Majalisar Dattawa ba.
Matan sun yi wannan barazana ne a lokacin da Ndume ya karbi bakuncinsu tare da sauran magoya bayansa a gidansa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A lokacin taron ne Sanata Ali Ndume ya bayyana sharadinsa na ci gaba da zama a Jam’iyyarsa ta APC.
Idan za tuna, uwar Jami’yyar APC na da hannu wajen tsige Ndume daga mukaminsa a Majalisar saboda ya soke Gwamnatin Shugaba Tinubu kan yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su a Najeriya.
- Zanga-zanga ’Yancin ’Yan Najeriya ne —Kungiyar Arewa
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Takaddama Kan Rushe Hukumomin Raya Biranen Kaduna
A kan haka ne kuma aka tsige shi daga mukaminsa Na mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi.
A wasikar da ta shugaban jam’iyyar Abdullahi Ganduje ya aika wa majalisar ya bukaci Ndume ya koma jam’iyyar adawa ya zaba wa kansa.
Amma a yayin jawabin Ndume a Maiduguri, ya bayyana cewa ba zai ci gaba zama a Jam’iyyar ne bisa sharadin muddin Gwamnan Borno, Babagana Zulum bai bar ta ba.
Nduma ya sanya zaman Zulum a APC a matsayin sharadin zamansa a jam’iyyar ne a Maiduguri, a lokacin da yake jawabi ga mata magoya bayansa.
Mata magoya bayan Sanata Muhammad Ali Ndume sun yi barazanar yin zanga-zanga tsirara a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa, idan ba a mayar da shi kan kujerunsa na shuagabanci a Majalisar Dattawa ba.
Ndume ya ce: “A kan kiran da kwamitin APC na kasa (NWC) ya yi cewa in bar jam’iyyar in koma wata jam’iyyar, to Allah Ne kadai Ke ba da mulki ga wanda Ya so.
“Saboda haka, ina so in bayyana cewa ina daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC.
“A halin yanzu, jagoranmu Gwamna Zulum yana APC, kuma duk inda Gwamnanmu yake, nan nake.”
Da yake magana a madadin kungiyoyin, Fasto Moni Mushari, ya ce suna goyon bayan Sanata Ndume kan “fadin gaskiya.”