✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi wa fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja yankan rago —Ansaru

Kungiyar Ansaru na barazanar ranar Laraba za ta fara yanka fasinjojin jirgin kasan da ke hannunta.

Kungiyar Ansaru ta yi barazanar fara yi wa fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ke hannunta yankan rago.

A wani sauti da ya yi ta yawo a cikin dare kafin wayewar garin Laraba, an ji wasu da ake zargin ’yan kungiyar ne suna barazanar yi wa mutanen da ke hannunsu yankan rago saboda gwamnati ba ta nemi a sake su ba.

Mawallafin jarida kuma daya daga cikin masu shiga tsakani domin a sako fasinjojin, Tukur Mamu, ya tabbatar da sahihancin sautin, da cewa kungiyar na barazanar cewa ranar Laraba za ta fara yi wa mutanen yankan rago. 

Ya ce “Sun fusata ne ranar Litinin bayan wata dama da suka ba mu.

“Ina kuka ina rokon su cewa tunda an samu jinkiri daga gwamnati, me zai hana su tattauna da iyalan mutanen kan yadda za a sako su, bayan nan ne suka amince su fara tattaunawa da iyalan.

“Amma sun ce sun ba mu zuwa ranar Laraba, idan ba a yi wani abu kwakkwara ba daga bangaren masu son a sako mutanen, za su yanka wasu daga cikinsu,” inji shi.

A ranar 28 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kai harin bom kan wani jirgin kasa da yake hanyar zuwa Kaduna daga Abuja, suka kashe mutane kimanin 1o suka yi garkuwa da wasu sama da 50, ciki har da mata da kananan yara da wani dan kasar waje.

Daga bisani sun sako 13 daga cikin mutanen, amma suka ci gaba da rike sauran.

A makon jiya Aminiya ta kawo cewa wani dan kungiyar ya harbi daya daga cikin fasinjojin da ke hannunsu, amma kungiyar ta ce ‘a bisa kuskure ne’.