Maharba a Jihar Taraba sun yi tayin bayar da taimako ga jami’an tsaro domin kawo karshen satar mutane a jihar.
Shugabar mata maharba a karkashin kungiyar maharba ta jihar, Malama Habiba Isa Hassan ta bayyana haka, inda ta ce maharban a shirye suke su taimaka wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen yaki da masu satar mutanen.
Malama Habiba Hassan ta shaida wa wakilinmu a garin Jalingo cewa maharba a shirye suke su bayar da gudunmawarsu wajen yaki da masu satar mutane amma fa sai jami’an tsaron sun gayyace su.Ta ce maharban jihar ba sa jin dadin yadda ake sace mutane a jihar musamman a kananan hukumomin Gassol da Bali inda matsalar ta fi kamari.
Malama Habiba ta ce matsalar satar mutane ta yi kamari a jihar, kuma ya kamata a taimaka wa jami’an tsaro wajen kawo karshenta. “Mu mata maharba a shirye muke mu bayar da duk taimakon da ya kamata wajen yaki da masu satar mutane a jihar. Sau daya aka nemi taimakon maharba a jihar nan a lokacin da masu satar mutane suka sace dan uwan wani dan siyasa a garin Jalingo. Kuma da taimakon maharba aka karbo wanda aka sacen ba tare da an yi wa wanda aka sace lahani ko biyan kudin fansa ba,” inji ta.
Ta ce akwai bukatar gwamnati da jami’an tsaro a jihar su sa maharba a cikin aikin tabbatar da tsaro musamsam wajen yaki da masu satar mutane, saboda maharba sun fi kowa alaka da daji.
Shugabar ta ce mata suna bayar da gudunmawa mai yawa wajen magance matsalar tsaro a kasar nan musamman ganin yadda sarauniyar maharba daga garin Gombi a Jihar Adamawa ta shiga cikin jami’an tsaro masu yaki da Boko-Haram, inda ta taka muhimmiyar rawa a wannan fuska.
Malama Habiba ta ce tana kai kawo don ganin mata masu yawa sun shiga kungiyar maharban domin su bayar da gudunmawarsu ta fuskar tsaro a Jihar Taraba da kasa baki daya.