Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar Naira.
Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ne ya yi alkawarin yayin tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gefen taron kasar da kasashen Afirka da yake gudana a Riyadh, babban birnin kasar.
- Yakin Gaza: Tinubu ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta
- Gaza: Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da Hamas
Saudiyya ta kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya, ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), domin a farfaɗo da darajar Naira.
Yarima Muhammad, a cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya kuma yabawa manufofin tattalin arzikin da Shugaba Tinubu yake aiwatarwa.
A cewar Yariman na Saudiyya, ƙasar shi ta ƙagu ta ga Najeriya tana bunkasa a karkashin Shugaba Tinubu, musamman a matsayinta na jagaba a Afirka.