✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu shafe Tel Abib daga bayan kasa idan Isra’ila ta kawo mana hari – Iran

Wani jami’in kasar Iran ya ce, kasarsu za ta shafe birnin Tel Abib daga bayan kasa kuma ta kasha Firayi Ministan kasar Benjamin Netanyahu idan…

Wani jami’in kasar Iran ya ce, kasarsu za ta shafe birnin Tel Abib daga bayan kasa kuma ta kasha Firayi Ministan kasar Benjamin Netanyahu idan shugaban na Isra’ila ya cika alkwarinsa na kai wa Iran hari.

Sakataren Majalisar Kyautata Rayuwar Jama’a ta Iran, Mohsen Rezaee ya shaida wa kafar labarai ta Al-Manar a ranar Litinin cewa: “Game da kalaman wauta na Netanyahu, abin da zan ce idan ya kuskura ya aikata rashin kan gado ga Iran, za mu mayar da Tel Abib turbaya, kuma ba za mu bar kafar da Netanyahu zai gudu ba.”

Majalisar ce take ba Shugaban Addini na Iran, wanda shi ne yake nada wakilanta.

Wannan barazana tana zuwa ne a lokacin da zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya kan rawar da Iran take takawa a Syria da Yemen da kuma yadda Shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da matsawa kan a dauki tsauraran matakai a Iran, yayin da a nata gefen Isra’ila ke dada neman goyon baya domin dakile abokan gabanta na yankin.

 A karshen makon jiya kasashen biyu sun yi ta musayar zafafan kalamai a wajen taron Zaman Lafiya na Duniya a birnin Munich.

Netanyahu ya gabatar da birbishin abin da ya kira jirgin leken asirin kasa na Iran da sojinsa suka kakkabo bayan ya kutsa a sararin samaniyar Isra’ila a farkon wannan wata, inda ya ce: “Isra’ila ba za ta bari a kai mata harin ta’addanci har cikin gidanta ba, kuma za mu dauki mataki idan ya zama wajibi ba a kan yaran Iran ba, a kan ita kanta.”

Sai dai Rezaie ya yi watsi da jawabin inda ya ce, surutan banza ne da was an yara kamar yadda kafar labarai ta FARS ta ruwaito. Ya ce: “Shugabannin Amurka da Isra’ila har yanzu ba su san Iran ba, kuma ba su fahimci karfin turjiya ba, kuma za su ci gaba da shan kasa.”