Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar.
Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Haka kuma, ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbin kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100.
Alƙaluma dai sun tabbatar da cewa an samu gagarumar faɗuwa a jarawabar JAMB da aka rubuta a wannan shekara.
A yayin da JAMB ke ƙayyade mafi ƙanƙantar makin samun gurbin karatu, ita ma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami’o’in ƙasar.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wannan Talatar a yayin taron tsara fitar da guraben karatu na 2025 a ƙasar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Za a shigar da ƙa’idar cika shekara 16 a cikin manhajar Hukumar JAMB da ke tantance ƙa’idojin bayar da gurbin karatu.
Haka kuma, Ministan ya ce za a yi la’akari da ɗaliban da za su cika shekara 16 ranar 31 ga watan Agustan 2025.
A bayan nan dai ana ta cece-kuce kan bai wa ƙananan yara guraben karatu a jami’o’in ƙasar, wani abu da masana ke cewa zai shafi fahimtarsu da kuma yadda za su iya jure wa wahalhalun karatun jami’a.