✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A soke sakamakon jarabawar JAMB na 2025 gaba ɗaya —Ɗalibai

Sama da ɗalibai miliyan 1.5 sun kasa samun maki 200 a jarabawar UTME na 2025 da Hukumar JAMB ta gudanar

Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum.

Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar.

Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya.

A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai.

Sai dai a ranar Laraba Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa ls-haq Oloyede ya kira taron ’yan jarida, inda ya amsa cewa hukumar ta gano cewa laifinta ne, ya kuma ba da haƙuri kan kurakuran da aka samu a jarabawar.

Farfesa Oloyede wanda a yayin jawabin ya fashe da kuka ya bayyana cewa hukumar ta gano haka ne bayan ta sake nazari kan sakamakon jarabawar. Ya ce yawan ƙorafin jama’a ya sa hukumar ta hanzarta yin bitar jarabawar da wuri, maimakon ta jira har sai lokacin da ta saba yi a watan Yuni.