Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar an samu kura-kurai a sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan.
A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Oloyede, ya fashe da kuka yayin da yake bai wa ɗalibai haƙuri, inda ya nuna nadamarsa kan wahalar da suka sha.
- Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe
- ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara
A cewar JAMB, matsalolin fasaha sun shafi sakamakon ɗalibai 379,997.
Waɗannan matsaloli sun fi shafar jihohin Kudu maso Gabas da kuma Jihar Legas.
A Legas, ɗalibai 206,610 daga cibiyoyi 65 ne suka fuskanci matsalar, yayin da ɗalibai 173,387 daga jihohi biyar na Kudu maso Gabas suka fuskanci irin wannan matsala a cibiyoyi 92.
Baya ga kura-kuran, mafi yawan ɗaliban da suka zana jarrabawar ba su samu makin da ake buƙata ba.
Daga cikin sama da ɗalibai miliyan 1.96 da suka rubuta jarrabawar, sama da miliyan 1.5 sun samu maki ƙasa da 200 daga cikin maki 400.
Ƙalilan daga cikin ɗaliban ne suka samu maki sama da 300.
Wannan sakamako ya tayar da hankali kan matsayin ilimi da yadda ake shiryawa ɗalibai jarrabawa.
JAMB ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan matsalolin fasaha da suka auku, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa faruwar hakan nan gaba.