✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi

Sakamakon bana ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.

Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu ta JAMB a bana.

Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi.

Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki sakamakon na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon haka a kalle shi a matsayin yadda ɗaliban da suka ci suka nuna hazaƙa lokacin rubuta jarabawar.

“JAMB na gudanar da jarabawarta ta hanyar amfani da tsarin kwamfuta wato CBT.

“Sun ɗauki ƙwararan matakai da ya janyo aka samu raguwar satar amsa matuƙa,” in ji shi.

“Saboda haka daga shekara mai zuwa muna so duk wata jarrabawar ɗalibai masu kammala sakandire ta koma tsarin amfani da komfuta.”

A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da sanawar fitar da sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.

JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.

Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.

A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.

Rukunin da ya fi yawan ɗalibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu ɗalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 ke nan.

Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.

Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 sun gaza samun ko da maki 100.