More Podcasts
Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban.
Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME.
Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar sun samu ƙasa da maki 200.
Ko waɗanne dalilai ne suke kawo faɗuwa jarabawa a Najeriya?
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?
- DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
Wannan shi ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi ƙoƙarin amsawa.
Domin sauke shirin, latsa nan