✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu sanya wa jam’iyyu ido kan kudaden yakin neman zabe — INEC

INEC ta kuma ce za ta sa ido kan kalaman batanci

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sha alwashin sanya ido kan harkokin yakin neman zaben jam’iyyu da yadda za su rika kashe kudadensu gabanin zaben 2023.

Hukumar ta ce za ta yi hakan ne don tabbatar da cewa ba su saba wa doka tanadin doka ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wajen taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.

Yakubu ya kuma ce za su sanya ido kan jam’iyyun domin tabbatar da ba su yi amfani da kalaman batanci ba, da kuma kiyaye ka’idar kashe kudi don zabe.

Ya kara da cewa, abin da Dokar Zabe ta 2022 ta tanadar shi ne, jam’iyyu su fara gangamin neman zabe a bainar jama’a kwana 150 kafin ranar zabe, wanda tuni an bude kofar hakan ranar 28 ga watan Satumba.

Ya ce za a ci gaba da kamfe na takarar Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisar Tarayya har zuwa ranar 23 ga Fabrairun 2023, sannan zuwa tara ga watan Maris din 2023 ga ’yan takarar Gwamna da ’yan majalisun jihohi.

A cewar Yakubu, daga yanzu zuwa kwanaki 148 masu zuwa, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu na da damar karade kasa baki daya tare da yin tarurruka don neman kuri’a a wajen jama’a.

Ya ce, “Ana iya tattaunawa da su, yada bayanai da tallata harkokinsu a gida da waje. Galibi irin wannan lokaci, lokaci ne mai tattare da farin ciki da zumudi ga jami’yyu da magoya bayan nansu.”

Daga nan Shugaban na INEC ya ja hankalin ’yan siyar kan su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da yin la’akari da ka’idojin da aka gindaya musu.

(NAN)