Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce za ta rufe rajistar masu kada kuri’a a ranar 31 ga watan Yulin da muke ciki.
Babban Kwamishinan INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.
- Kotu za ta saurari shari’ar halasta wa Ganduje karbo bashin Naira Biliyan 10
- Sunayen kwalejojin kiwon lafiya 26 da gwamnatin Kano ta rufe
Matakin na zuwa ne bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta kori karar da Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci ta shigar gabanta.
Kungiyar ta SERAP dai na neman kotun ta tilasta wa INEC kara wa’adin rajistar da ke gudana a fadin kasar.
Okoye ya ce kotun ta tabbatar da cewa INEC na da damar sanya ranar rufe rajistar kamar yadda sabuwar Dokar Zabe ta 2022 ta tanada.