✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni

Za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen daga ranar 27 ga watan Mayu har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2025.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar.

Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin sunayen ’yan takara za su gudana daga ranar 25 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, 2025.

Shugaban ya ce, za a maido da jerin sunayen ’yan takarar da aka tura musu daga ranar 3 zuwa 10 ga Afrilu yayin da za a wallafa bayanan ’yan takarar daga ranar 11 zuwa 18 ga Afrilu, 2025.

Ya ƙara da cewa an shirya tattara fom ɗin tsayawa takara a ranar 19 zuwa 26 ga Afrilu yayin da jam’iyyun siyasa za su gabatar da fom ɗin takara daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu, 2025.

Ya ce, za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen daga ranar 27 ga watan Mayu har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2025.

Imam ya tabbatar wa jam’iyyun siyasa matakin da za a yi na gudanar da zaɓuka cikin ’yanci, gaskiya da adalci bisa wasu dokoki da jagororin gudanar da zaɓukan kansiloli.