Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba da umarnin kwace takardun filayen duk bankin da ke kin ba wa mutanen jiharsa sabbin tardun Naira da aka canza.
Zulum ya ba da umarnin ne bayan an gagara samun takardun sabbin kudi na Naira 100,000 a fadin Karamar Hukumar Gubio ta jihar.
- Yadda take kayawa a muhawarar ’yan takarar Gwamnan Kano na Media Trust
- Canji kudi: Manoma sun ki sayar wa ’yan kasuwa amfanin gona
Ya ce, “Duk bankin da ya yi ki loda sabbin kudin a ATM domin mutanenmu su samu, za mu kwace takardun filinsa.”
“Ragon da a baya ake sayarwa N100,000 ya koma N35,000 saboda yadda mutane ke neman tsabar kudi ido rufe, sannan wasu maara imani na shiga kauyuka suna cutar muane,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya bayyana bacin ransa ne bayan ya iske dogon layin mutane a reshen wani banki wanda ATM guda daya tal daga cikin ATM da ke reshen ne ke ba da kudi.
“Na je ATM sun fi 1o, amma daya kadai ke da kudi,” in ji shi.
“Rashin sabbin kudin da ma ofaffin na shafar harkokin kasuwanci a jihar, kuma jama’a na shan wahala,” in ji Zulum.
“Ba mu da matsala da tsarin CBN ko kayyade cirar N20,000, tun da an ce kowa zai iya cirar N20,000 to me zai hana kowa samu?” in ji shi.
Don haka gwamnan ya rokin Babban Bankin Najeriya ya yi abin da ya dace wajen abbaar da wadauwar sabbin ukarudin kudaden ga ’yan kasa.