Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa game da sake haduwa da ƙara ƙarfin mayakan Boko Haram a yankunan Tumbus na Tafkin Chadi da kuma tsaunukan Mandara a cikin dajin Sambisa.
Yayin da yake jawabi ga Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da manyan hafsoshin soji a Maiduguri, Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addancin Boko Haram a Borno da ma yankin Arewa maso Gabas, amma ya nuna wani abin damuwa da ya faru kwanan nan a ayyukansu.
Ya bayyana cewa bayan an yi ayyukan soja an gama, sai sojojin su janye, sai kuma ’yan Boko Haram da ISWAP su sake dawowa su karɓe waɗannan yankunan da aka ƙwato a baya.
Babban abin da gwamnan ke damuwa da shi shi ne rashin gudanar da ayyukan soja a cikin ruwan Tumbus na Tafkin Chadi. Ya bayyana yankin a matsayin maɓoyar da ’yan ta’adda ke samun sauƙin samun kayan aiki har ma da ƙaruwar.
- ’Yar Arewa da ta kafa tarihin samun Digiri Mai Daraja ta ɗaya a fannin Shari’a
- Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
- Ƙarin ’yan Najeriya za su shiga talauci nan da 2027 — Bankin Duniya
Ya jaddada buƙatar gaggawar sojoji su gudanar da ayyuka a cikin waɗannan ruwayen, saboda yana zama mafaka ga ’yan ta’adda da ke aiki a duk faɗin Arewacin Najeriya.
Gwamna Zulum ya kuma jaddada matuƙar buƙatar ƙarin sojoji don daƙile manyan yankuna masu wahalar shiga kamar yankin Timbuktu, Tumbus, tsaunukan Mandara, da kuma iyakar Najeriya da ke da ramuka da ƙasashen Sahel.
Duk da fahimtar cewa sojoji sun bazu a faɗin Najeriya, ya roƙi a ƙara tura ƙarin ƙwararrun sojoji zuwa Arewa maso Gabas, yana mai jaddada goyon bayan ƙasashen waje da kuma yadda ake shigowa ta yankin Sahel wanda ya bambanta Boko Haram da ISWAP da ’yan fashi.
Ya bayyana cewa tabbatar da tsaro a yankin Sahel yana da matuƙar muhimmanci ga tsaron Najeriya gaba ɗaya, kuma ya yi kira da a ci gaba da gudanar da ayyukan soja.
Gwamnan ya roƙi a ƙara samar da ƙarin kayan aikin soja masu ƙarfi, kamar tankoki, motocin yaƙi na MRAP, da harsasai, tare da muhimman tallafin jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙi.
Ya ma lura cewa harin da aka kai kwanan nan a Wulgo an ce an kai shi ne da taimakon jirage marasa matuƙi masu ɗauke da makamai, don haka ya roƙi sojoji da su sayi jirage marasa matuƙi masu inganci da kayan aikin kare kai.
Bayan ayyukan soja, Gwamna Zulum ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin da ba na yaƙi ba, yana mai nuna cewa Jihar Borno ta karɓi fiye da ’yan Boko Haram 300,000 da suka tuba a cikin shekaru uku da suka gabata, kuma yawancinsu ba mayaƙa ba ne, manoma ne kawai.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Gwamna Zulum ya nuna kyakkyawan fata kuma ya yi alƙawarin ba da cikakken goyon baya ga sojoji a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen ta’addanci. Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da shugabannin soji bisa ga irin goyon bayan da suke ba al’ummar Jihar Borno.
Da yake mayar da martani ga damuwar gwamnan, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta ƙara tallafin soja don magance sabbin ƙalubalen tsaro a Borno da Arewa maso Gabas. Ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya ba su umarni da su samar da duk wani abin da ake buƙata don dakatar da wannan yanayin damuwa.
Ministan Tsaron ya amince da zaman lafiya da Jihar Borno ta samu a baya-bayan nan saboda ƙoƙarin gwamnan da kuma yadda mutane da yawa suka koma gidajensu da ƙauyukansu don sake gina rayuwarsu.
Ya yi alƙawarin cewa za a magance matsalolin tsaron da suka taso kwanan nan waɗanda ke barazana ga nasarorin da aka samu a baya-bayan nan cikin gaggawa, kuma gwamnati na daraja shawarwari da tunanin gwamnan wajen ƙarfafa dabarunsu na kawo ƙarshen rashin tsaro.