Ashekaranjiya Laraba ce Jaridar Punch ta wallafa ra’ayinta mai taken “Karya Doka Daga Buhari: Matsayinmu,” inda ta ce ta yanke shawara daga yanzu za ta rika kiran Shugaba Buhari da lakabinsa na soja na Janar da kuma bayyana salon mulkinsa da na kama-karya.
Jaridar ta ce ta yanke wannan shawara ce saboda abin da ta kira da i‘keta hakkokin dan Adam’ da Shugaba Buhari ke yi a kasar nan, al’amarin da jaridar ta ce ya sha bamban da salon mulkin dimokuradiyya.
A cewar jaridar, “A wani matakin nuna rashin amincewarmu ga salon mulkin kama-karya da na soja, jaridar Punch daga yanzu za ta fara makala wa Buhari tsohon matsayinsa na soja na Manjo Janar wanda yake amfani da shi lokacin mulkin soja a shekarun 1980. Sannan za mu rika bayyana gwamnatinsa da ta danniya, har zuwa lokacin da ya fara mutunta dokokin kasa,” kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito.
Jaridar ta zayyana wasu dalilanta da ta ce su ne suka ba ta damar ayyana gwamnatin Buhari da ‘kama-karya’ da ‘rashin mutunta doka da oda’, kamar haka;
i. Batun “kama dan jaridar nan na Sahara Reporters, Omoyele Sowore da jami’an Hukumar DSS aka ce sun yi a cikin kotu.
ii. Yadda ’yan jarida suke fuskantar kalubalen fadin albarkacin bakinsu.
iii. Kokarin hana jama’a fadin albarkacin bakinsu a kafofin sadarwa na zamani
ib. Kamawa da tsare ’yan kasa fiye da awa 48 da jami’an tsaron kasar nan ke yi a karkashin Gwamnatin Buhari.
b. Yadda Gwamnatin Buhari ke ci gaba da tsare tsohon Mai ba Shugaban Kasa Jonathan Shawara kan Tsaro, Kanar Sambo Dasuki da jagoran Kungiyar IMN da gwamnati ta haramta, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
bi. Irin yadda jami’an DSS suka yi wa alkalai dirar mikiya a gwamnatin Buhari,
Dokar Najeriya ce ta bada damar kiran Buhari Shugaba– Garba Shehu
Da yake mayar da martani, Kakakin Shugaban Kasa Buhari, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa “jaridar Punch ta koma jaridar siyasa.”
Garba Shehu ya kara da cewa “Jaridar tana magana ce a kan kama Omoyele Sowore wanda shi kuma ya yi kira da a yi juyin juya-hali bayan da ya fadi a zaben Shugaban Kasa.Saboda haka shi Omoyele Sowore dan siyasa ne ba dan jarida ba.”
Dangane kuma da batun kiran Buhari Shugaban “kama-karya”, Malam Garba Shehu ya ce “dokar Najeriya ce ta bayar da damar kiran Buhari Shugaban Kasa.”
A game da ko za su dauki wani mataki, sai ya ce, “Babu wani matakin doka da za mu dauka illa mu bar su da ’yan Najeriya su yi hukunci, tunda su ne suka zabi Shugaba Buhari har karo biyu.”