✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu hukunta duk wanda ya ki karbar tsoffin kudi —Ganduje

Ganduje ya ce ba za su yi kasa a guiwa wajen hukunta duk wanda ya ki karbar tsoffin takardun kudi.

Gwamnatin Jihar Kano, ta yi gargadin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwace lasisin wasu manyan ‘yan kasuwa ko kuma daukar mataki kan duk wanda ya ki karbar tsofaffin takardun kudi.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce har yanzu tsoffin takardun Naira ana ci gaba da amfani da su.

Ya ce Kotun Koli ta yanke hukuncin wucin gadi na tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin Naira har zuwa ranar da za ta yanke hukunci.

Gwamnan ya ce ba za su lamunci yadda wasu ‘yan kasuwa, manyan kantuna, bankuna, gidajen abinci, otal-otal, kasuwanni, gidajen mai, da wuraren ajiye motoci, da dai sauransu ke kin karbar tsofaffin takardun kudin ba.

Ganduje ya kara da cewa rashin amincewa da kudin na kara dagula al’amura, kuma hakan na kara jefa mutane cikin tsaka mai wuya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ayyukan kasuwanci da na tattalin arziki sun yi matukar tasiri wajen sauya fasalin kudin Naira, kuma abin takaici wasu sun daina karbar tsofaffin kudi, lamarin da ya kara jawo wa jama’a wahala yayin gudanar da hada-hadarsu.

Ya ce jama’a sun sha wahala, don haka gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta ba ta bar wasu su kara ta’azzara lamarin ba.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu tare da kai rahoton duk wanda ya ki karban tsofaffin takardun Naira zuwa wuraren da suka dace.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar ta kulle babban kantin sayayya na ‘Well Care’ saboda kin karbar tsoffin takardun kudin Naira.