Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa , gwamnati zata gurfanar da duk masu yi wa zaman lafiya barazana a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da hukumar zaman lafiya ta jihar ta shirya akan hanyoyin gudanar zaben 2019 cikin lumana a jihar.
El-Rufai, ya ce, idan har hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar da sahihin zabe kamar na zaben Gwamnan jihar Osun, za a samu zaman lafiya a Kaduna lokacin zaben 2019 da bayan zaben.