Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya umarci jami’an tsaro cewa daga yanzu su fara rushe gidajen masu yi wa ’yan daban daji leken asiri da kuma masu taimaka musu wajen samun makamai.
Mai magana da yawun gwamnan, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da Matawalle ke karbar bakuncin takwaransa na Jihar Sakkwato, Aminiu Waziri Tambuwal da ’yan Majalisarsa, wanda suka kai masa ziyarar jaje dangane da hare-haren baya bayan da suka auku a wasu sassan jihar da ya janyo asarar rayukan mutane da dama.
A cewar gwamnan, ya ba da umarnin a dauki matakai masu tsauri ciki har da rushe gidajen duk wanda aka samu yana bai wa ’yan daban daji bayanai da kuma wadanda ke taimakonsu wajen samun nasarar kai hare-hare a sassan jihar.
Ya ce wannan mataki ya zama tilas domin dakile aukuwar hare-haren ’yan daban daji a yayin da ake samun wasu bata-gari daga cikin al’ummar jihar da ke basu gudunmuwa ta rura wuta wajen sheke ayarsu.
“Ayyukan masu taimakon ’yan daban daji yana kara rura wutar ta’addanci a jihar da haifar da matsala ga zaman lafiya a jihar,” in ji Matawalle.
Ya bukaci al’umma a jihar da su ba da gudunmuwa wajen ganin an murkushe ’yan daban daji, tare da umartar sarakunan gargajiya da su sanya idanun lura a kan dukkan al’amuran da ke faruwa a yankunan da ke karkashin ikon masarautunsu.