✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato

Al'ummar jihar na ci gaba da kokawa game da hare-haren 'yan bindiga.

Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana sunan mamatan a matsayin Umar Sa’idu da Rashida Yakubu.

Ya ce lamarin ya faru ne da yamma, kuma ya sanar da manyan jami’an tsaro ciki har da sojoji da ’yan sanda.

Babayo ya yi Allah-wadai da kisan, ya kuma roƙi hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don hana sake faruwar irin haka a gaba.

Ya kuma buƙaci ’yan uwansa Fulani da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa ɗaukar doka a hannu.

“Abin da ke faruwa da al’ummarmu yana da matuƙar tayar da hankali. Mun riga mun rasa shanu sama da ɗari tare da wasu makiyaya. Yanzu kuma an kashe mana wasu biyu,” in ji shi.

Sai dai wani jigo a ƙungiyar raya al’adu ta Bokkos (BCDC), John Apollos Maton, ya ce bai da labarin faruwar harin.

Ya kuma musanta cewa mutanensu na da hannu a lamarin, inda ya bayyana cewa su dai kawai suna kare kansun ne daga ’yan ta’adda.

Mai magana da yawun Rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai amsa tambayar da wakilinmu ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Tun da farko, Aminiya ta ruwaito cewa an kai hare-hare da dama ƙauyukan Bokkos tsakanin watan Maris da Afrilu, inda mutane da dama suka mutu.

Hukumomin tsaro sun tura jami’ansu domin wanzar da da zaman lafiya a yankin.