A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno.
Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai.
Rahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam.
An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji na hedikwatar Operation Hadin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya ya fitar ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta ce, lamarin na farko ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis a garin Buratai, inda ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kutsawa inda dakarun suke daga wurare da dama.
“Sojojin, duk da haka, cikin hanzari sun yi artabu da ‘yan ta’addan da manyan bindigogi, yayin da dakarun sama da manya-manyan Jiragen yakin Tucano suka ba da tallafi ta sama ga sojojin.”
Kyaftin Kovangiya ya bayyana daga bayan an gano gawarwakin ‘yan Boko Haram dama, tare da tarin makamai da alburusai iri-iri.
Hakazalika, sojojin a Mallam Fatori sun dakile wani harin da ‘yan tada kayar bayan suka tunkaro inda suke daga bangarori daban-dabam.
Sanarwar ta kara da cewa, “Sojojin sun yi wa ‘yan Boko Haram mummunan barna lamarin da ya sa su tserewa cikin rudani.”
Bayan da ‘yan tada kayar bayan da suka ja da baya ya kai ga kashe mutane da dama, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu a Mallam Fatori sun hada da: bindigogi kirar AK-47 da yawa, manyan bindigogi masu linzami (GPMGs), bindigogin roka (RPGs), da sauran kayan aikinsu na ta’addanci.