Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruq Yahaya ya ce dakarunsa sun shirya tsaf don kawar da dukannin ‘yan ta’adda da makiya kasar nan daga doron kasa.
Janar Yahaya ya bayyana haka ne a ziyarar bikin Ista da ya kai wa dakarun a barikin sojojoji na Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
- Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci saboda taurin bashi
- Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta —Fadar Shugaban Kasa
A jawabinsa, wanda kwamandan rundunar a yankin Arewa maso Gabas, Manjo-Janar IS Ali ya karanta, ya yaba da rawar da dakarun ke takawa wajen murkushe ’yan ta’adda tare da wargaza maboyarsu a duk yankin da ma Yankin Tafkin Chadi.
Babban Hafsan ya kuma yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa irin goyon bayan da yake bai wa dakarun kasar nan a fafutukarsu ta kawar da ’yan ta’adda a yankin da ma fadin kasar nan.
Wasu daga cikin mahalarta bikin sun hada da dakarun rundunar OPHK da sojojin da suka samu raunuka a filin daga wadanda yanzu suke murmurewa da sauran su.
Kazalika, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan Jihar Borno, Barista Malam Fannami, yayin da Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Dokta Abubakar Ibn Umar Garbai Al’amin El-Kanemi ya samu wakilcin Zanna Wawurma Na Masarautar Borno, Alhaji Usman Chiroma da sauran manyan baki.