✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama mutum 4 kan zargin ta’addanci a Taraba

Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne.

Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne.

Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin  suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar.

Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo.

Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin.

Kyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar kai ɗauki wurin, inda hakan ya kai ga kama mutanen huɗu, uku daga cikinsu na rike da makamai.

Ya ce makaman da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da bindigogi uku, adduna guda 3, alburusai guda 42, wayoyin hannu guda 4 da katin shaidar ƙasa guda 1.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani mai mutum da kiran wadannan mutanen zuwa yankin, kuma ana ci gaba da bincike kan rawar da ya taka a lamarin.