✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato

Ana fargabar an yi garkuwa da wasu daga cikin mafarautan da Lakurawa suka kashe 13 daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa Jihar Sakkwato

Tawagar haɗin gwiwar jami’an tsaro na aikin gano gawarwakin wasu mafarauta da mayaƙan Lakurawa suka kashe a yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato.

Ana fargabar Lakurawa sun yi garkuwa da wasu daga cikin mafarautan da suka fito daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa, bayan sun faɗa tarkon ’yan ta’addan.

Aminiya ta ruwaito cewa mayaƙan Lakurawa sun kashe mafarauta 13 a wani harin kwanton ɓauna, sannan suka tarwatsa wani turken sadarwa mallakar Kamfanin MTN a Ƙaramar Hukumar Tangaza.

’Yan ta’addan sun kai wa mafarautan farmaki ne a Dajin Hurumi da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza, a yayin da suka fita farautar shekara-shekara, wanda ya samu mahalarta daga wurare daban-daban.

Mafarautan sun yi arba da ’yan ta’addan ne da misalin Azahar na ranar Alhamis, duk da cewa hukumomi sun gargaɗe su dangane da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa farautan da ke ɗauke da bindigogi harbi-ruga, tare da rakiyar karnukansu sun tafi kai-tsaye ga maɓoyar ’yan ta’addan da ke cikin dajin.

Zuwa lokacin da muka samu wannan labari, wani mazaunin garin Tangaza da ya ƙi bayyana sunansa saboda tsaro ya ce, an gano gawarwaki uku, saura 10, sa’annan wasu da suka tsallake rijiya da baya kuma sun dawo gida.

Mazauna yankin sun bayyana cewa mamatan sun haɗa da mafarauta biyar daga ƙauyen Kangiye sai biyu daga Chancha da wasu biyu daga Rantijadi da biyu daga Gandaba Gabasa sai mutum ɗai-ɗai daga Gidan Kaji da kuma Gandaba Yamma.

Yadda sojoji suka ragargaji Lakurawa

A ranar Juma’a Lakurawa suka kai wani hari a ƙauyen Magonho da ke Laramar Hukumar Tangaza, amma sojoji suka kai ɗauk suka fatattaki ’yan ta’aɗɗan sa’annan suka ƙwato shanun jama’a da suka sace.

Cikin ƙasa da awa biyu Lakurawa suka kai wani harin bom, inda inda suka tarwatsa turken sadarwa mallakin Kamfanin MTN, lamarin da ya katse layin sadarwa a yankin.

Ana neman mafarautan da suka ɓace

Da yake tabbatar da kisan mafarauta a Tangaza, Mashawarci na Musamman kan Sha’anin Tsaro ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Ghazzali Aliyu Rakah, ya ce rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro da ’yan banga sun shiga dajin domin gano mafarautan da ba a gani ba.

Ya ce, “Tun ranar Asabar muke aiki, amma ƙarancin jami’an tsaro da motocin aiki sun kawo cikas. Amma mun samu ƙarin jami’an tsaro daga yankunan Raka, Tsauna, and Binji domin taimakawa.”

Ghazzali Aliyu Rakah ya ƙara da cewa mafarautan da tsautsayin ya rutsa da su ba aikin yaƙi da ta’addanci suka je ba, farautar shekara-shekara da suka saba yi ce ta kai su.

Ghazzali ya ce, “Suna sane da haɗarin amma suka zaɓi su shiga jeji farautar. Kaddara ce ta same su.

‘Lakurawa sun dasa nakiyoyi’

Ya yi gargaɗi cewa ’yan ta’addan sun tsananta amfani nakiyoyi da sauran abubuwan fashewa.

“A watan jiya wasu sojoji sun mutu bayan da motarsu ta taka wata nakiya. Wannan ya sa yanayin matsalar tsaronmu ta fi ta Isa da Sabon Birni muni,” in ji shi

Ya kuma koka bisa matsalar masu kai wa ’yan ta’adda bayanai, wadda ta kai ga “sojoji sun taɓa barazanar tashi daga sansaninsu a yankin saboda wannan cin amanar.”

Ghazzali Rakah ya ƙara da cewa ce ’yan ta’addan suka yi shigar burtu su saje a cikin jama’ar gari, wanda ke sa da wuya a gane su.

Za mu ɗauki mataki —Gwamnati

Da yake tabbatar da harin turken sadarwa na MTN, Ghazzali ya bayar ta tabbacin cewa gwamnatin jihar da ƙaramar hukumar suna aiki haiƙan domin wanzar da tsaro a Tangaza.

Mashawarci kan sha’anin Tsaro ga Gwamna Ahmad Aliyu, Kanar Ahmed Usman (Murabus) ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da–kafaɗa da hukumomin tsaro domin kare al’ummomin jihar.

“Gwamna ya ba da fifiko ga sha’anin tsaro kuma yana ɗaukar mataki nan take a duk lokacin da muka tuntuɓe shi. Amma duk da haka muna buƙatar samun goyon bayan jama’a, su daina bayar da mafaka ga masu laifi,” in ji Kamar Usman.

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da hare-haren tare da cewa an gano gawarwakin mafarauta biyu kuma ’yan uwansu sun riga sun yi musu jana’iza.

DSP Rufa’i ya ce cewa jami’an tsaro na ci gaba da aikin gano ragowar mafarautan da ba a gani ba.

Jerin hare-haren Lakurawa a Tangaza

Wannan hari ƙari ne a kan matsalar tsaron da ke ci wa yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza tuwo a ƙwarya.

A watan Afrilu Lakurawa sun kashe masunta biyu da wani manomi da suka yi nusu kwanton ɓauna a yayin da suke yin su a ƙauyen Sanyinna.

Kafin nan a watan Maris ’yan ta’addan sun kai farmaki ƙauyen Baidi, inda suka kashe mutum ɗaya tare da jikkata wani soja da fararen hula uku, sannan suka sace garken raƙumma da wasu dabbobi.

A yayin arangamarsu da sojoji daga baya an samu asarar rayuka daga ɓangarorin biyu.

Muna samun nasara — Sojoji

Duk da wannan ƙalubale Babban Kwamandan Rundunar ta 8 ta Sojin Najeriya, Manjo-Janar Ibikunle Ajose, ya bayyana ƙwarin gwiwar game da nasarar sojoji.

A jawabinsa ga dakarunsa a watan Janairu a yayin bikin Wasanni na Ƙasashen Afirka (WASA) na 2025, Ajose ya bayyana cewa, “ana samu tsayayyar nasara akai-akai a yaƙi da ta’addanci.

“Sojojinmu sun kashe shugabannin ’yan ta’adda da dama da kuma mayaƙansu, wanda hakan ya sa aka ci gaba da gudanar da ayyukan noma da sauran harkokin tattalin arziki a jihar.”

Ya alaƙanta nasarar da sabbin kayan yaki da jiragen da rundunar ke amfani da su, yana mai jaddada cewa sojoji za su ci gaba da aiki ba dare, babu rana domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya a kowane lokaci har sai zaman lafiya ya wanzu a ƙasar.

‘Sun so yi wa sojoji tarko da mafarauta’

Wani jami’in ƙaramar hukumar da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun so su yi amfani da mafarautan a matsayin farkon da za su yi amfani da su wajen yi wa sojoji kwanton ɓauna.

Ya ce, “Lakurawa sun so ne su yi amfani da mafarautan domin su faruwa sojoji, amma ba mafarautan ba ne ainihin hadafinsu.”

Ya ce amma sojoji sun farga bayan samun bayanan sirri a yankin, saboda, “muna musayar bayanai da sojoji shi ya sa ba su faɗa a tarkon zuwa yankin ba.”

Ya bayyana cewa mafarautan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Gwada awa da Tangaza, yana mai cewa, “mun samu labarin an yi garkuwa da wasubdaga cikinsu, kuma muna ƙoƙarin gano ko suna da rai ko an kashe su.”

Lakurawa sun sauya salo —Jami’in gwamnati

Ya ƙara da cewa Lakurawa sun sauya salo a cikin ’yan watannin da suka gabata.

Ya ce, “Yanzu sun dai ƙaƙaba wa mutanen ƙauyuka dokokinsu yadda suke yi a baya. Sun fi mayar da hankali kan satar dabbobi da kai wa jami’an tsaro hari, domin ƙwace makamansu.”

Aminiya ta samu labarin cewa ƙungiyar ta zagaye maɓoyar mayaƙansu da nakiyoyi da suka bibbinne a kan hanyar zuwa sansanin nasu.

“Kusan babu wani yanki a Tangaza da ba su shiga ba, in banda Masallaci and Rakah da ke da sansanonin soji. Amma gundumar Salewa gaba ɗayanta a ƙarƙashin ikonsu take,” a cewar jami’in.

Ya bayyana cewa yanayin ya jefa mazauna cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

“Ƙaramar Hukumarma na fama matsananciyar matsalar kuɗaɗe. Muna tallafa wa ayyukan samar da tsaro, har ta kai ga yanzu bashi ya yi mana jariri,” a cewar majiyar.

Wani mazaunin Tangaza ya bayyana damuwa bisa yadda Lakurawa ke cin karensu babu babbaka a yankunan karkara.

Ya ce, “Su ba kamar sauran ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suke ba. Sun mayar da hankali ne a kan jami’an gwamnati da jami’an tsaro da satar shanu. Sukan far wa fararen ne kawai idan an take su ko aka yi musu Turkiya.”