✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masana sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje

Wani kwararre a kan sha'anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce  bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin tsaron…

Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue.

Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa.

Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman.

Wani kwararre a kan sha’anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce  bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin tsaron iyakokin Najeriya da masu tara bayanan sirri.

n kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da makamai suka kai a kwanakin baya.

Manjo-Janar Kangye ya ce duk da cewa ana magana da Hausa a sassa daban-daban na Afirka, amma abu mai sauƙi ne a gane waɗanda ba ’yan Najeriya ba ne. Ya ce, “idan aka ji su suna magana, za a iya gane ’yan ƙasa ne ko baƙi.”

Ya bayyana cewa sun kama wasu daga cikin ’yan ta’addan, kuma yadda suke magana da kamanninsu da ma gashin kansu, yana nuna cewa ba ’yan Najeriya ba ne.

Y amince cewa yawancin masu aikata ta’addanci a Najeriya baƙi ne, duk da cewa akwai ’yan ƙasar a cikinsu. Ya ƙara da cewa yawancin tashin hankalin da ake ji a wasu sassan ƙasar nan, galibi waɗanda suka shigo ƙasar ta bayan fage ne ke aikata su.

Ya yi kira ga hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro don tabbatar da an yi ɗauki bayanan duk wanda ya shigo Najeriya.

Masana sun ɗiga ayar tambaya

Sai dai, wasu masana tsaro sun nuna shakku game da wannan iƙirarin.

Dakta Kabiru Adamu, Shugaban Kamfanin Beacon Consult, ya amince cewa sojojin Najeriya suna fuskantar matsin lamba sosai saboda ƙaruwar hare-hare da kuma yadda ake bibiyar su daga kafafen yada labarai da manyan jami’an gwamnati.

Ya ce wannan matsin lamba zai iya shafar ƙarfin guiwar sojoji da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu, wanda zai iya kai su ga bayar da irin wannan sanarwa don nuna cewa suna samun ci gaba tare da ɗora alhakin ga wasu.

Ya yi nuni da yarjejeniyar ECOWAS kan zirga-zirgar dabbobi da makiyaya, yana mai cewa duk da manufarta ta sauƙaƙa zirga-zirga, ana ganin ta a matsayin hanyar da ’yan bindiga za su iya shigowa kasar ba tare da an san su ba.

Kabiru Adamu ya yi kira da a sake duba yadda ake aiwatar da wannan yarjejeniya tare da samar da hanyoyin da za a iya bibiyar masu shigowa ƙasar.

Ya kuma jaddada matsalar iyakar Najeriya da ba ta da tsaro, yana mai kira da a inganta haɗin gwiwa da ƙasashe makwabta tare da saka hannun jari a yankunan kan iyaka.

Wani tsohon kwamandan sojin sama, Dakta Musa Salmanu, ya ce zai ɗauki maganar kakakin hedikwatar tsaro da muhimmanci, amma ya nuna damuwa cewa idan ’yan kasashen waje ne ke kai hare-haren, hakan na nufin Najeriya na fuskantar wani nau’i na mamayewa.

Ya yi tambayoyi game da ko waɗannan mutane ne suka zo da kansu ko kuma wasu ƙasashe ne ke ɗaukar nauyinsu.

Ya jaddada cewa ko ’yan Najeriya ne ko baƙi, babban abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za a dakatar da barnar da suke yi.

Ya kuma yi kira da a magance tushen matsalar rikicin makiyaya da manoma da sauran matsalolin tsaro a sassan Najeriya.

Wani tsohon ɗan majalisa, Destiny Enabulele, ya zargi shugabannin Najeriya da rashin jajircewar magance matsalar rashin tsaro.

Ya yi tambaya game da yadda ake kashe kuɗaɗen da aka ware don tsaro, yana mai cewa har sai an samu jajircewar yaƙar rashin tsaro, ba za a samu mafita ba.

Ya kuma yi kira ga jami’an shige da fice da na kwastam da su koma kan iyakokin kasar don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Wani masanin tsaro, Jackson Lekan Ojo, ya musanta iƙirarin sojojin, yana mai cewa hakan ya nuna gazawar hukumomin iyaka da na leƙen asiri na ƙasar.

Ya ce ya kamata a hukunta waɗanda ke da alhakin tsaron iyakokin Najeriya, yana mai bayyana ikirarin a matsayin “uzuri maras tushe,” da ke nuna halin ko-in-kula na sojoji da sauran jami’an tsaro.

Ya yi kira da a fatattaki waɗannan mutane, a kama su ko kuma a mayar da su kasashensu.