Rahotonni na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai kashe dakaru huɗu yayin wani hari da suka kai sansanin soji a Jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na “27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Gujba da tsakar daren Asabar.
- Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato
- Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato
Harin na zuwa ne kwana guda bayan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabashin ƙasar sun gudanar da taro a Damaturu, babban birnin jihar da nufin magance matsalolin yankin, ciki har da matsalar tsaro.
A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na neman dawo da hare-hare a yankin.
A cikin makon nan ma ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 26 a Jihar Borno.
Ko makonni biyu da suka gabata sai da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke yankin Chalie a Ƙaramar Hukumar Buni Yadi, inda suka kashe dakaru uku.
Sai dai a bayan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙwato dazukan Arewa da ma sauran sassan ƙasar daga hannun masu garkuwa mtane domin karɓar kuɗin fansa da ‘yan ta’adda