Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan diyyar masu taron Mauludin da harin bom daga jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da haka, sa’o’i kadan bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin.
Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Harin dai ya auku ne a lokacin da wata makatar Islamiyya take gudanar da bikin Mauludi a daren Lahadi a kauyen Tudun Biri, inda ta karbi bakuncin mahalartar daga kauyukan da ke kusa da su.
- Mutum 85 sun rasu, 66 sun jikkata a harin Kaduna —NEMA
- Harin Mauludi: Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike
Ana tsaka da taron ne wani jirgi mara matuki mallakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya yi mahalarta taron ruwan bama-bamai.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 85 a harin baya ga wasu 66 da suka samu raunuka.
’Ya’yana 6, duk an kashe su —Magidanci
Wani matashi dan Tudun Biri, Idris Dahiru, ya ce, a mutum 34 aka kashe a cikin danginsu a harin.
“Wannan jirgi ya kashe al’ummarmu maza da mata da yara a danginmu mun rasa mutum 34,” in ji Idris.
Ya bayyana cewa a cikin minti 30, jirigin ya jefa musu bom sau biyu.
Wani magidanci, Malam Musa, ya ce kanana 12 a gidansu harin ya kashe, ciki har da ’ya’yansa shida, maza uku da mata uku, da kuma ’ya’yan ’yan uwansa guda shida.
Shi ma wani Kirista da ya rasa ’ya’yansa biyu a harin, Solomon John ya ce ’ya’yan nasa na cikin Kiristoci uku da aka kashe a harin.
Ya ce yaran nasa, Kiristoci ne, amma suka halarci taron Mauludin, inda a nan suka gamu da ajalinsu.
Sarkin Garin Tudun Biri, Malam Suleiman Shu’aibu ya ce akasarin wadanda suka rasu a harin, yara ne da mata.
Ya bayyana cewa al’ummar garin sun saba gudanar da tarukan Mauludi ba tare da wata matsala ba, sai a wannan karon.
Sarkin kauyen Ifira, daya daga cikin kauyukan da harin ya ritsa da mutanensu a taron, Malam Balarabe Garba, ya yi kira ga gwamnati ta biya diyyar wadanda harin jirign sojin ya shafa.
Al’umma da kungiaoyi na ci gaba da kira ga gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya faru, da nufin hana aukuwar irin haka a nan gaba.
Hakazalika wasu na kira da gano jami’in da ke da laifin harin a hukunta shi, domin ya zama darasi ga wasu.
Ba da gangan ba ne —Shugaban Sojin Kasa
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa harin na Tudun Biri ba bisa ganganci rundunar ta kai shi ba.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin wata ganawa da Shugaban Kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna, Farfesa Shafi’u Abdullahi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban na JNI ya bayyana fatan sojojin za su dauki matakan da suka dace wajen hana sake faruwar hakan.
Laftanar-Janar Lagbaja, wanda shi ne tsohon Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa da ke Kaduna, ya roki Allah Ya yi wa wadanda suka rasu rahama.
Lagbaja ya jaddada cewa a lokacin da yake aiki a Kaduna, ya jagoranci ya jagoranci rundunar yaki da yan ta’addanci kuma ba a samu irin wannan tsautsayin ba.
Ya kara ba da tabbacin cewa runduanr ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinta na tabbatar da tsaron kasa.