✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 85 aka kashe, 66 sun jikkata a harin Kaduna —NEMA

Tuni Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike.

Akalla mutum 85 ne suka mutu a harin jirgin sama da sojojin Najeriya suka kai a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) na shiyyar Arewa maso Yamma, Halima Suleiman ce, ta bayyana hakan, inda ta ce mutum 66 da harin bam din ya rutsa da su sun jikkata.

Ta ce kididdigar wadanda suka mutu ya samo asali ne daga mahukuntan yankin bayan jana’iza a ranar Litinin.

“Ofishin shiyyar Arewa maso Yamma ya samu cikakken bayani daga hukumomin yankin cewa kawo yanzu an binne mutum 85 yayin da ake ci gaba da bincike,” in ji NEMA.

Sai dai kuma jami’an agajin na ci gaba da tattaunawa da shugabannin al’umma domin kwantar da hankalin jama’ar yankin.

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gudanar Da Bincike

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin yin cikakken bincike kan kisan masu taron Mauludin wanda ya yi ajalin mutane da dama.

A safiyar Talata shugaban kasar ya ba da umarnin a cikin sakon ta’aziyyarsa game da rasuwar mutanen da tsautsayin ya auka musu.