✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen daliban da aka sace a Jami’ar Tarayya a Zamfara sun yi zanga-zanga

Iyayen daliban da aka sace a Jami’ar Tarayya da ke Gusau sun yi zanga-zangar lumana a gidan Gwamnatin Zamfara suna neman a sako ’ya’yansu

Iyayen daliban da aka sace a Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar, suna neman a sako ’ya’yansu ba tare da wani sharadi ba.

Sun bukaci Gwamna Dauda Lawal da jami’an tsaro su ceto ’ya’yansu da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 72 ba tare da wani abu ya same su ba.

Masu zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da zama a gidan gwamnatin Jihar Zamfara har sai an sako ’ya’yansu.

Sun ce ’yan bindigar sun tuntubi wasu daga cikinsu kuma sun bayar da sharadin tattauanawa da gwamnatin jihar kafin sakin daliban.

A ranar 22 ga watan Satumba ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da daliban jami’ar kimanin 24 tare da wasu ma’aikata a jami’ar.

Sai dai an kubutar da dalibai 13 da ma’aikatan gini uku yayin da har yanzu raguwar suke tsare a hannun ’yan bindigar.