✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi zaman makokin kwana 3 kan kisan mutum 50 a Burkina Faso

An ware ranakun don jimamin wadanda suka rasa rayukansu

Gwamnatin mulkin soja a Burkina Faso ta sanar da zaman makoki na tsawon kwana uku daga ranar Talata bayan da mahara suka kashe mutum 50 a Arewacin kasar.
Shugaban mulkin sojin kasar, Laftanar-Kanal Paul-Henri Damba, ne ya bayar da umarnin yin zaman makokin ranar Talata.
A ranar Litinin ne gwamnatin kasar ta ce an kashe farar hula 50 a wani hari da wasu mahara da ake zargin ’yan tawaye ne suka kai a yankin Seytenga, inda gwamnatin ta ce akwai yiwuwar adadin mutanen zai iya karuwa.
Wasu rahotanni sun ce adadin mutanen da suka rasu ya kai zarta 50.
A lokacin zaman makokin, gwamnati ta ce za a rage tsawon tutar kasar a kusan duka gine-ginen gwamnati da kuma ofisoshin jakadancin kasar a kasashen waje.