Fitattacen Malamin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi gargadi cewa gwamnatin Najeriya ta yi hattara da ayyana ’yan bindiga a mastayin ’yan ta’adda.
Sheikh Gumi ya bayyana haka ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci Shugaba Buhari ya amince da bukatar Majalisar Dokoki ta ayyana ’yan bindiga a matasyin ’yan ta’adda domin sojoji su samu damar kashe su ba tare da fargabar keta wata doka ba.
- Sudan: Sojoji sun ayyana dokar ta-baci, sun tsare shugabannin kasar
- Buhari sam ba ya nema ko daukar shawara —Ghali Na’Abba
Gumi ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Abubuwan da ’yan bindinga ke aikatawa a yankin Arewa maso Yamma na ta’addanci ne, tunda har mutanen da babu ruwansu ba su bari ba.”
Sai dai ya ce ayyana su matsayin ’yan ta’adda na bukatar a yi hattara sosai, saboda hakan na iya sa wasu kungiyoyin ta’adda su nemi hadewa da su, musamman masu fakewa da addini, wadanda kuma ke iya jan ra’ayin matasa marasa aikin yi.
“Kowa da yadda yake ganin adalci. Idan har ana ganin ba laifi ba ne a kashe matansu da ’ya’yansu saboda dangantakarsu da su, to su ma ’yan bindigar na iya irin wannan tunani.
“Ana ganin ba laifi ’yan banga su karkashe duk wani Bafulani ko mai kama da su saboda an bata musu suna, amma kuma ba daidai ba ne su su rama.
“Hakan ke sa su yi tunananin cewa yakar su ake yi domin a shafe su daga doron kasa, kuma a yaki, babu batun wata ka’ida ko tsari.”
Gumi ya ce, “Saukinta shi ne babu wani mai sha’awar shiga cikinsu a yankin Arewa, saboda kabilanci da suka sanya a lamarin.”