✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a tura ’yan sanda 21,000 don tabbatar da zaman lafiya a zaben Osun

Ya ce jami'an za su tabbatar da zaman lafiya

Babban sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce za a tura jami’an ’yan sanda 21,000 don tabbatar da zaman lafiya a zaben Gwamnan Jihar Osun da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a Osogbo, babban birnin jihar ta Osun, yayin taron masu ruwa da tsaki a hedkwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta jihar.

Sai dai Babban Sufeton ya ce ba wai za a aike da jami’an tsaron ba ne don firgita masu zabe, sai don tabbatar da cewa bata-gari ba su yi amfani da zaben wajen tayar da zaune tsaye ba.

Ya ce girke jami’an zai tabbatar da samar da tsaro, ya kare masu kada kuri’a, ma’aikata da kayan zaben, kafin, yayin da kuma bayan kammala zaben.

Usman Alkali ya ce tuni aka horar da jami’an kan hanyoyin da za su bi wajen gudanar da ayyukan nasu, inda ya ce za su tabbatar ba su yu katsa-landan ga harkar zaben ba.

Da yake nasa jawabin, Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce hukumarsa ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata don gudanar da zaben.

Ya ce tuni suka aike da da kayan zabe ga dukkan ofisoshin zaben na Kananan Hukumomin Jihar.

Farfesa Mahmud ya ce za a aike da muhimman kayan zabe gundumomin siyasa na jihar awa 24 kafin lokacin zabe, yayin da za a ci gaba da raba katin zabe har zuwa ranar Alhamis, 14 ga watan Yulin 2022.

A bangaren katinan zabe kuwa, ya ce daga cikin mutum 1,955,657 da suka yi rajista a jihar, 1,479,959 sun karbi katinan zabensu ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata.

(NAN)