✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu

An gano waɗanda suka yi safarar ne da ake zargin suna shirin fitar da shi zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa'ida ba.

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya (Kwastam), ta ce ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da mazaƙutar jakai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumar ta Kwastam ta sanar da kama motar ne a ranar Alhamis.

An gano waɗanda suka yi safarar ne da ake zargin suna shirin fitar da shi zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa’ida ba.

An samu nasarar ne a ranar Juma’a 5 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9 na dare, bayan wani haɗin gwiwa da jami’an ofishin kula da namun daji na musamman da na hukumar Kwastam suka gudanar.

Kwaturola Janar na Hukumar kwastam, Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Maimagana da yawun hukumar ta Kwastam, Abdullahi Aliyu Maiwada wanda ya wakilci Kwanturola Janar na Kwastam ya bayyana cewa, nasarar kama masu aikata hakan na cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile kasuwancin dabbobin dawa ta ɓarauniyar hanya.